9 Mayu 2020 - 06:13
​An Sake Gano Wasu Dala Miliyan 319 Da Abacha Ya Boye A Kasashen Turai

Gwamnatin Amurka ta sanar da gano wasu sabbin makudan kudade na dala miliyan 319, kwatankwacin naira biliyan 121, da ta ce tsohon shugaban Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha ya boye a kasashen Burtaniya da kuma Faransa.

(ABNA24.com) Gwamnatin Amurka ta sanar da gano wasu sabbin makudan kudade na dala miliyan 319, kwatankwacin naira biliyan 121, da ta ce tsohon shugaban Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha ya boye a kasashen Burtaniya da kuma Faransa.

Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa,Cikin sanarwar da ya fitar, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce dala miliyan 167 na boye a Faransa, yayin da dala miliyan 152 ke a Burtaniya.

Gano sabbin kudaden ya zo ne kasa da mako guda bayan da Amurka ta mika wa Najeriya dala miliyan 311 da ake tuhumar tsohon shugaban Najeriyar marigayi Janar Sani Abacha ya boye su a cikin wani banki da ke kasar ta Amurka.

Gwamnatin Najeriya ta kwashe tsawon shekaru tana fafutukar karbo kashin farko na dala miliyan 311 daga Amurka, da ake zargin tsohon shugabanta a zamanin mulkin sojan ya boye.


/129